Isa ga babban shafi

Faransa za ta fara ladabtar da masu sauya tunanin jama'a a shafukan sada zumunta

Masu sauya wa mutane tunani a shafukan sada zumunta na fuskantar barazanar dauri a gidan yari ko kuma a ci su tarar makuden kudade karkashin wata sabuwar doka da Majalisar Dokokin Faransa ta amince da ita. 

Karkashin sabbin dokokin Faransa za ta rika daurewa ko kuma cin tarar wadanda aka samu da laifin sauya tunanin jama'a a shafukan sada zumunta.
Karkashin sabbin dokokin Faransa za ta rika daurewa ko kuma cin tarar wadanda aka samu da laifin sauya tunanin jama'a a shafukan sada zumunta. © AP / Tommy Martino
Talla

Asali dai an samar da wannan dokar ce domin ladabtar da masu yada tallace-tallace ba bisa ka’ida ba da kuma ‘yan damfara a shafukan sada zumunta. 

Tun a cikin watan Maris da ya gabata ne, kudirin dokar ya samu goyon bayan mabanbantan jam’iyyun da ke zauren Majalisar Dokokin Faransa. 

An kiyasta cewa, akwai kimanin mutane dubu 150 da ke da matukar tasiri a shafukan sada zumunta a Faransa kuma da dama daga cikinsu na da miliyoyin mabiya, abin da ya sa suke samun karbuwa a bangarorin da suka shafi tallar kayan ado da wasannin nishadi. 

Mafi yawancin tallace-tallacen da suke kambamawa  da ke kawo musu tarin kudi a lalitarsu, sun saba wa ka’idojin shari’a a Faransa. 

Yanzu haka sabuwar dokar za ta tilasta musu su rika fayyace wa mabiyansu cewa, lallai wannan sakon da suka wallafa a shafinsu nada nasaba da talla ko kuma hadin guiwar kasuwanci da suka karbi kudi a kai. 

Kazalika sabuwar dokar ta haramta tallar  man shafe-shafe mai sauya fasalin halitta da taba sigari da kayayyakin asibiti da kuma caca da dai sauransu. 

Duk wanda ya karya sabuwar dokar, zai iya zaman gidan yarin shekaru biyu da kuma biyan tarar Euro dubu 300. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.