Isa ga babban shafi

Ukraine na bukatar karin taimakon manyan makamai daga Turai- Macron

Shugaban Faransa Emmanuel Macron, ya ce akwai bukatar kasashen Turai su kara bai wa Ukraine tabbaci a bangaren tsaro a daidai lokacin da kasar ke fuskantar mamaya daga Rasha. 

Shugaba Emmanuel Macron na Faransa.
Shugaba Emmanuel Macron na Faransa. AFP - LUDOVIC MARIN
Talla

A lokacin da yake tattaunawa da manema labarai a gefen taron da ya samu wakiltar kasashe 47 mafi yawansu daga Turrai, wanda ya gudana jiya alhamís a kasar Moldavia, Macron ya sanar da cewa kungiyar tsaro ta NATO, za ta gudanar da taro a cikin watan gobe a garin VIlnus na Lithuania don tattauna batun na Ukraine.

 

Macron ya bayyana cewa sakon da gabaki dayansu su ke son aikewa Rasha shi ne, ta fahinci cewa kawunansu a hade ya ke sannan kuma za su ci gaba da taimaka wa Ukraine da kuma al’ummarta. 

Shugaban na Faransa ya bayyana cewa domin ganin cewa kasar ta mayar da martani da nufin kwato yankunanta, lalle Ukraine na bukatar samun tabbaci na tsaro, tare da mutunta dokokin kasa da kasa. 

Ina da yakinin cewa, taron Vilnus, zai dauki mataki tare da fitar sako walihan zuwa ga al’ummar Ukraine, kuma ya zama wajibi a dauki wannan mataki domin tabbatar da tsaron Ukraine da kuma al’ummarta a cewar Macron. 

Matakin da taron na kungiyar NATO zai gudanar, shi ne zai kara fayyace manufarmu ga kasar Rasha. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.