Rasha ta girke makamin nukiliya a Belarus don afka wa Ukraine
Shugaban Belarus Alexander Lukashenko ya bayyana cewa, Rasha ta fara girke makaman nukiliya a cikin kasar wadda ke zama makwabciyarta kuma aminyarta, matakin da ke zuwa bayan shugaba Vladimir Putin ya sanar da wannan shirin a cikin watan Maris.
Wallafawa ranar:
Kawo yanzu babu sanarwar da Rasha ta fitar da kanta da ke nuna cewa, lallai ta fara jibge makamanta na nukiliya a makwabciyar kasarta ta Belarus.
Sai dai shugaba Lukashenko ya shaida wa taron manema labarai a yayin wata ziyara da ya kai birnin Moscow cewa, an fara aikewa da makaman na nukiliya.
Shugaban na Belarus ya ce, takwaransa na Rasha, Putin ya shaida massa cewa, tun a ranar Laraba, ya sanya hannu kan dokar izinin girke makamin na nukiliya.
Lukashenko dai ya bai wa Rasha kan iyakar kasarsa domin ta zama wani sansanin kaddamar da farmaki cikin Ukraine.
Belarus na da iyaka da Ukraine da kuma kasashen Poland da Lithuania da suka kasance mambobi a Kungiyar Tarayyar Turai da kuma Kungiyar Tsaro ta NATO.
A cikin watan Maris ne shugaba Putin na Rasha ya sanar cewa, zai girke makamin nukiliya mai cin garejen zango a kan iyakar Belarus, lamarin da ya janyo masa caccaka daga kasashen yammacin duniya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu