Isa ga babban shafi

MDD ta kafa gidauniyar dala biliyan 1 don taimakon wadanda girgizar kasa ta shafa a Turkiya

Majalisar dinkin duniya ta kaddamar da gidauniyar dala biliyan guda a don taimaka wa wadanda iftila’in girgizar kasar da ta kashe dubban mutane ta shafa a Turkiya.

Magatakardan Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres.
Magatakardan Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres. © ONU
Talla

A wata sanarwa, babban magatakardan majalisar dinkin duniyaAntonio Guterres ya ce za yi  amfani da kudaden da za a tara ne don samar da agaji ga sama da mutane miliyan 5 da iftila’in ya rutsa da su.

Ya kara da cewa kudaden za su taimaka wa kungiyoyin agaji wajen samar da gudummawa ta fannin abinci, ruwan sha, da matsugunai.

Akasarin yankunan da wannan girgizar kasa ta shafa na  cikin matukar bukatar agaji, inda suke fama da rashin abinci, ruwansha da makewayi.

Ya zuwa yanzu sama daa mutane dubu 38 ne suka mutu a wannan girgizar kasa a Turkiya kawai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.