Isa ga babban shafi

Ana ci gaba da zakulo masu rai kwanaki biyar bayan girgizar kasa a Syria da Turkiya

Masu aikin ceto na ci gaba da lalube a karkashin baraguzan gine-gine, yayin da aka shiga kwanaki na biyar bayan da mummunar girgizar kasa ta afkawa kasashen Turkiyya da Syria, da ya yi sanadiyar mutuwar sama da mutane dubu 21.

Wani gini da girgizar kasa ta shafa a Syria. 09/02/23
Wani gini da girgizar kasa ta shafa a Syria. 09/02/23 © Khalil Ashawi / REUTERS
Talla

A halin da ake cike dai, kayayyakin agajin farko na Majalisar Dinkin Duniya ya isa yankunan da ke hannun ‘yan tawayen Syria ranar Alhamis to sai dai an fara fidda tsammanin samun masu sauran numfashi a karkashin gine-gine saboda zarce adadin kwanaki ukun da kwararru ke bayyana su amatsayin lokacin da ya dace da aikin ceton rayuka.

Sanyi na kawo cikas ga ayyukan ceto

To sai dai saboda yanayi na tsananin sanyi da ke kawo cikas ga masu aikin ceto, ana ci gaba da samun masu sauran numfashi tsakanin kasashen biyu jifa-jifa. Sama da sa’o’i 80 bayan aukuwar bala'in, an gano Melda Adtas wata yarinya mai shekaru16 da ranta a birnin Antakya na kudancin Turkiyya.

Hotunan bidiyo sun nuna Mahaifinta cike da farin ciki yana zubda hawaye.

A cikin daren Litinin girgizar kasar mai karfin kusan maki  8 ta afkawa kasashen Turkiya da Syaria daidai lokacin da al’umma ke cikin barci a wasu yankunan tuni dama suke dandana kudarsu masu tarin ‘yan gudun hijira sakamakon yakin basasar Syria.

Amurka ta sassauta wasu takunkumi ga Syria

Amurka ta sanar da agajin dala biliyan 85 ga kasashen Turkiya da Syria wadanda ibtila’in girgizar kasa ya afkawa a farkon makon nan, tare da sassauta wasu daga cikin takunkuman da ke kan Syria don bayar da damar kaiwa kasar agaji. 

Cikin wata sanarwa da hukumar agaji ta Amurka USAID ta fitar ta bayyana cewa kayakin agajin da suka kunshi na abinci da matsugunan wucin gadi da kuma magunguna za su isa ga yankunan da ake bukata cikin gaggawa a kasashen biyu. 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.