Isa ga babban shafi

Wadanda suka mutu a girgizar kasar Turkiya da Syria sun doshi dubu 20

Masu aikin ceto a kasashen Turkiya da Syria na ci gaba da aikin zakulo masu sauran numfashi a karkashin gine-gine cikin tsananin yanayin sanyi, yayin da adadin wadanda mummunar girgizar kasar ta kashe ya doshi dubu 20

Wani yankin Turkiya da aka samu girgizar kasa mafi muni. 9/02/23
Wani yankin Turkiya da aka samu girgizar kasa mafi muni. 9/02/23 REUTERS - SUHAIB SALEM
Talla

Duk da cewar akwai karin fargabar adadin mutanen da suka mutu sakamakon girgizar kasar na tun ranar Litinin mai karfin kusan maki 8 ya karu sosai kwararru kan bala'o'i na ganin akwai dama ga masu aikin ceto wajen nasarar kara samun masu rai a karkashin baraguzan gine-gine saboda yayin sanyi mai dauke da dusar kankara .

Wata mata na zaune a kan baraguzan gine-gine a yayin da tawagar agajin gaggawa ke neman mutanen da ke karkashin buraguzan gine-gine a garin Nurdagi da ke wajen birnin Osmaniye a kudancin kasar Turkiyya, Talata, 7 ga Fabrairu, 2023.
Wata mata na zaune a kan baraguzan gine-gine a yayin da tawagar agajin gaggawa ke neman mutanen da ke karkashin buraguzan gine-gine a garin Nurdagi da ke wajen birnin Osmaniye a kudancin kasar Turkiyya, Talata, 7 ga Fabrairu, 2023. AP - Khalil Hamra

Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan da ya kai ziyar gani da ido wasu yankunan kasar da iftila’in yafi kamari a Laraban nan ya na fuskatar suka daga ‘yan kasar kan yadda ake tafiyar da aikin ceto kan girgizar kasar mafi muni cikin fiye da karni.

Suna zargin an bar wadanda suka tsira da ransu wajen neman abinci da matsuguni da kansu,  yayin da a wasu lokuta suna ji suna ganin yadda makusantansu ke bukatar agaji a karkashin gine-gine daga bisani sai adaina jin duriyarsu.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.