Adadin wadanda suka mutu a girgizar kasar Turkiya da Syria ya zarta dubu 11
Masu aikin ceto a Turkiyya da Siriya dake fama da tsananin sanyi na ci gaba da aikin gano masu sauran numfashi a karkashin gine-ginen da girgizar kasar ta rutsa da su , yayin da adadin wadanda suka mutu ya zuwa yanzu ya haura dubu 11.
Wallafawa ranar:
Girgizar kasar mafi muni da kasashen suka gani cikin shekaru da dama ya kara haifar da tabarbarewar al’umara a yankin kan iyakar da dama can ke fama da rikici, yayin da wadanda suka tsari daga iftila’in da yanzu haka ke rayuwa a kan tituna ke kona tarkace a kokarinsu na samun dumi saboda tsananin sanyi gami da dusar kankara.
Yayin da taimakon kasashen duniya suka fara isa, masu aikin ceto na kokarin zakulo masu sauran numfashi, kuma cikin nasarar da suke samu ana ganin abubuwan al’ajabi da ban tausai, ciki harda yadda aka ciro wani jariri da rai daga baraguzan gine-gine a Siriya, wanda alamu suka nuna cewa ba’aji da haihuwarsa ba saboda ko cibiyarsa na hade da ta mahaifar sa wacce ta mutu.
Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya ayyana dokar ta baci na tsawon watanni uku a larduna 10 da lamarin yayi kamari.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu