Isa ga babban shafi

Mutanen da girgizar kasa ta kashe a Turkiya da Syria sun doshi dubu 3

Adadin mutanen da suka rasa rayukansu sakamakon girgizar kasa a kasashen Turkiya da Syria ya zarta dubu 2 da 700, yayin da ake ci gaba da aikin ceto mutanen da suka makale karkashin buraguzai.

Wani bangare da ya ruguje sakamakon girgizar kasar a Turkiya.
Wani bangare da ya ruguje sakamakon girgizar kasar a Turkiya. © AP
Talla

An bayyana girgizar kasar a matsayin mafi muni da aka gani cikin kusan shekaru 100 a wannan yanki, yayin da alkaluma ke nuni da cewa, akalla mutane dubu 1 da 762 ne suka mutu a Turkiya kadai, inda adadin ya kai dubu 1 da 300 a Syria.

Akwai yiwuwar samun karin mamata nan gaba, ganin cewa, ana ci gaba da gudanar da aikin zakulo mutanen da suka makale a karkashin buraguzan gine-gine.

Tuni kasashen duniya suka gaggauta bada agaji tare da tura ma’aikatansu don gudanar da aikin ceto, yayin da Majalisar Dinkin Duniya ta yi shiru na tsawon minti guda domin karrama mutanen da suka mutu a ibtila’in.

Wasu hotunan bidiyo da aka yi ta yadawa a shafukan sada zumunta sun nuna yadda dogayen gine-gine ke nutsewa cikin karkashin kasa, inda kura ta turnuke manyan hanyoyi, sannan  mutane na ta neman tudun-mun-tsira.

Shugaban Turkiya Recep Tayyip Erdogan ya ayyana zaman makoki na tsawon kwanaki 7 a fadin kasar domin nuna alhini ga mutanen da wannan mummuan ibtila’in ya rutsa da su.

Shugaban ya ce, za a yi kasa-kasa da tutar kasar a tsawon kwanakin 7 na zaman makoki.

 

 

 

 

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.