Isa ga babban shafi

Stoltenberg zai sauka daga shugabancin kungiyar tsaro ta NATO

Shugaban kungiyar tsaro ta NATO Jens Stoltenberg ya sanar da shirin sa na ajiye aiki a watan Octoba mai zuwa, abinda ya haifar da cece-kuce game da wanda zai gaje shi.

Shugaban kungiyar tsrao ta NATO
Shugaban kungiyar tsrao ta NATO AP - Markus Schreiber
Talla

Sai dai kuma mahukuntan kungiyar tarayyar turai sun ce har yanzu babu wata tattaunawa da aka yi a hukumance game da wanda zai gaji tsohon Prime ministan kasar Norway Jens Stoltenberg.

To amma kuma wasu na ganin cewa akwai alamun za’a karawa shugaban wa’adin sa, bayan shafe tsahon shekaru 9 yana jagorantar kungiyar, a kokarin da ake yi na kawo karshen yakin Russia da Ukraine.

Sai dai duk da wannan kuma mai Magana da yawun na Stoltenberg Oama Lungescu ta kuma tabbatarwa da manema labarai cewa a watan October mai zuwa ne Stoltenberg zai sauka daga mukamin sa na jagorantar kungiyar ta NATO.

Sau uku ana karawa shugaban wa’adin jagorancin kungiyar kuma a jimlace ya shugabanci NATO na tsahon shekaru 9, yayin da wa’adin mulkin nasa zai kawo karshe a watan Octoban shekarar da muke ciki, Kuma mai Magana da yawun nasa ta jadadda cewa bashi da sha’awar sake karbar wani karin wa’adi.

Tuni dai masu nazari game da siyasar turai suka fara ganin da wannan sanarwa masu sha’awar gadon buzun tsohon dan shekaru 63 zasu fara yunkurin samun kujerar da ke taka rawa wajen tabbatar da tsaron turai.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.