Isa ga babban shafi

NATO ta ce akwai bukatar a duba tashar nukiliyar Ukraine cikin gaggawa

Hukumar da ke sa ido kan makaman nukiliya ta Majalisar Dinkin Duniya za ta duba tashar makamashin nukiliya ta Zaporizhzha a Ukraine da ke karkashin ikon sojojin Rasha.

Babban jami’in kungiyar tsaro ta NATO, Jens Stoltenberg kenan tare da shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky
Babban jami’in kungiyar tsaro ta NATO, Jens Stoltenberg kenan tare da shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky © New Europe
Talla

Babban jami’in kungiyar tsaro ta NATO, Jens Stoltenberg wanda ya bayyana hakan ga manema labarai a Brussels ya ce kame tashar da Rasha ta yi na haifar da babbar barazana ga tsaro tare da haifar da hatsarin ga shirin kera makaman nukiliya.

Akwai bukatar bayar da izinin gaggawa domin gudanar da binciken hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa da kuma tabbatar da janyewar dukkan sojojin Rasha a yankin.” a cewar babban jami'in na NATO.

Karbe ikon wurin da sojojin Rasha suka yi " barazana ce mai girma ga al'ummar Ukraine, da kasashe makwabta da kuma saurar sassan kasashen duniya," in ji Stoltenberg.

A cikin watan Maris ne sojojin Rasha suka kwace tashar makamashin nukiliya ta Zaporizhzhia, dake kudancin Ukraine, jim kadan bayan mamayar da suka yiwa kasa a watan Fabrairu.

Cibiyar nukiliyar ita ce mafi girma a Turai, kuma rashin tabbas da ke tattare da shi a yayin da ake gwabza yaki ya haifar da hatsari ga shirin nukiliyar wanda ake ganin zai fi na Chernobyl da aka samu a shekara ta 1986, lokacin da wani makamin mai ya fashe.

Rasha da Ukraine sun zargi juna da harba makamin nukiliya ga yankin na Zaporizhzhia.

A makon da ya gabata ne kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya gudanar da wani taron gaggawa kan lamarin inda ya yi gargadin game da wani babban rikici mai cike da hatsari da ya kunno kai a birnin Zaporizhzhia.

A ranar Alhamis ne Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres zai tattauna a yammacin Ukraine tare da shugaban kasar Volodymyr Zelensky da shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan. Ana sa ran tattaunawar za ta hada da batun cibiyar nukiliyar ta Zaporizhzhia.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.