Isa ga babban shafi

Ukraine zata samu karin makamai bayan mummunar harin Rasha - NATO

Kungiyar tsaro ta NATO ta bayyana cewa Ukraine na jiran tsammanin karin wasu manyan makamai daga kasashen yammacin duniya nan ba da dadewa ba, yayin da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya yabawa dakarunsa bayan da suka yi ikirarin kwace wani gari na Ukraine.

Ana aikin ceto a Ukraine bayan harin Rasha a Dnipro
Ana aikin ceto a Ukraine bayan harin Rasha a Dnipro © REUTERS / CLODAGH KILCOYNE
Talla

Sanarwar NATO ta ranar Lahadi na zuwa ne yayin da ake gudanar da wani gagarumin aikin ceto a wani hasumiya da ke gabashin birnin Dnipro, sakamakon harin makami mai linzami da Rasha ta kai wanda ya yi sanadin mutuwar mutane akalla 30 tare da bacewar wasu 34.

Shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelensky ya yi Allah wadai da yadda kasashen duniya suka yi gum kan harin, yana mai cewa Ukraine bata samu sakonnin juyayi daga sassan duniya kan wannan ta'addanci ba.

Sakatare Janar na kungiyar tsaro ta NATO Jens Stoltenberg ya ce Ukraine na iya sa ran karin manyan makamai biyo bayan bukatar da Kyiv ta yi wa kawayenta na motocin yaki, manyan bindigogi da makamai masu linzami da ta ce suna da muhimmanci wajen kare kanta.

Stoltenberg ya shaida wa jaridar Handelsblatt ta Jamus cewa, "alƙawuran baya-bayan nan na samar da manyan kayan yaƙi na da mahimmanci -- kuma ina sa ran za a samu ƙarin a nan ba da dadewa ba."

Kwace birnin Soledar

Kwanaki bayan da Rasha ta yi ikirarin cewa ta kwace garin Soledar dake gabashin Ukraine, mai arzikin gishiri mai mutane 10,000 kafin rikicin, Putin ya yaba matakin a matsayin gagarumin nasara.

Ukraine ta musanta ikirarin Moscow, tana mai jaddada cewa ana ci gaba da gwabza kazamin fada a Soledar.

Amma a ranar Lahadin da ta gabata, Cibiyar Nazarin Yaki da ke Amurka ta ce "da wuya sojojin Ukraine su ci gaba da iya kare garin na Soledar ".

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.