Isa ga babban shafi

An sake zaben Marie-Christine Saragosse don shugabancin France Medias Monde

Marie-Christine Saragosse, shugabar France Médias Monde ta sake lashe kujerar shugabancin France Medias Monde, wacce musamman ta hada tashar talabijen na labarai ta Faransa 24 da gidan rediyon RFI, ta yi takara da wasu mutane hudu.

Marie-Christine Saragosse, shugabar France Médias Monde
Marie-Christine Saragosse, shugabar France Médias Monde RFI
Talla

Tun a shekarar 2012,uwargida Marie-Christine Saragosse, mai shekaru 62, ta sabi ragamar shugabanci  na tsawon shekaru biyar, bayan haka ta sake samu wani sabon wa’adi na shekaru biyar.

 France Médias Monde ta hada da tashar labarai France 24 (cikin Faransanci, Ingilishi, Larabci da Spaniya), rediyon RFI (cikin Faransanci da wasu harsuna 15) da kuma gidan rediyon harshen Larabci Monte Carlo Doualiya (MCD).

Marie-Christine Saragosse ta yi takara da mutane guda hudu,wanda kowa ya kawo nasa sani a bangaren da ya shafi sauye-sauye,tare da kawo sabon numfashi  a cikin rukunin jama'a, ga baki dayan su sun kuma  yin watsi da jinkirin da ake tsammani a fagen dijital da kuma sukar tsarin gudanarwa na yanzu.

Marie-Christine Saragosse, shugabar France Médias Monde
Marie-Christine Saragosse, shugabar France Médias Monde © rfi

Daya daga cikinsu, Sylvain Attal (tsohon mataimakin darektan France 24 mai kula da sabbin kafafen yada labarai) ya ba da tabbacin cewa 'yan jarida da yawa" daga Faransa 24 sun taka gaggarumar rawa a fanponi da da dama.

A cikin aikinta, Uwargida Marie-Christine Saragosse ta dage kan dangantakar amincewa  tare bada labarai masu inganci da  gaskiya ga jama'a, labaren  kasa da kasa masu zaman kansu  bisa gaskiya a wannan lokaci da ake fuskantar jita-jita daga wasu kafofin .

Kasafin kudin France Médias Monde yana karuwa a wannan shekara ta 2023 zuwa Yuro miliyan 285 akan 254 a 2022, yanayin da take son ganin ya tabbata kama daga  2024 zuwa 2028.

Bayan samun lasisin sauke nauyin da ke wuyan ta, Marie-Christine Saragosse  ta yi la'akari da cewa yana da mahimmanci a ci gaba da samun kuɗin da nufin watsa shirye-shirye  ga jama'a ta hanyar yin amfani da kudi da aka keɓe na musamman, ba kai tsaye ta kasafin kuɗin kasa ba.

Marie-Christine Saragosse, shugabar France Médias Monde
Marie-Christine Saragosse, shugabar France Médias Monde France 24

An dakatar da RFI da France 24 a cikin watan Afrilun da ya gabata a Mali, a wani yanayi na tada jijiyar wuya tsakanin Paris da Bamako. An kuma dakatar da RFI a Burkina Faso tun watan Disamba, Marie-Christine Saragosse ta kuma kare yawan harsunan da ake watsa shirye-shirye da su,a ƙarshe, ta nuna bukatar ta zuwa ga yuwuwar sauyawa zuwa tsarin dijital da sauraron buƙatuwata alama na biyawa da dama daga cikin masu saurare bukatun su a duniyar labarai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.