Isa ga babban shafi

Su waye suka lashe gasar Claude Verlon da Ghislaine Dupont ta RFI?

A ranar Laraba ne, wato 2 ga watan Nuwamba, Radio France International ya sanar da sunayen wadanda suka cancanci samun guraban samun horo karo na 9, da ake bayarwa domin karrama ma’aikatan RFI biyu wato Claude Verlon da kuma Ghislaine Dupont, wadanda ‘yan bindiga suka kashe ranar 2 ga watan Nuwambar shekara ta 2013 lokacin da suke gudanar da aikinsu a yankin Kidal da ke arewacin kasar Mali.

Wadanda suka lashe gasar Ghislaine Dupont ta RFI
Wadanda suka lashe gasar Ghislaine Dupont ta RFI © RFI
Talla

Sakamakon gasar ta bana dai na nuni da cewa Esther Senpa Blaksmedi ‘yar jarida da ke aiki da CRTV  a yankin arewacin Kamaru da kuma Henintsoa Tiana Miranto RAKOTOMALALA, injiniya a Aceem Radio da ke Madagascar ne suka yi nasara.

Wannan na nufin cewa mutanen biyu, za su amfana da horo na tsawon makonni 4 a birnin Paris, tare da daukar nauyinsu a watanni ukun farkon shekara 2023.

Daraktar gudanarwa ta RFI wato Cécile Mégie ce ta sanar da sakamakon gasar a lokacin wani muhimmin biki da ya gudana a birnin Dakar na kasar Senegal.

Gasar wadda ita ce karo na 9, an bai wa ‘yan jarida daga kasahen Afirka 25 da ke amfani da harshen faransanci damar nuna bajintarsu, kuma sama da mutane 300 ne suka shiga gasar ta wannan shekara.

Yadda aka zabo wandanda suka yi nasara

Bayan tankade da rairaye, an zabi kwararrun matasa 20 da suka fito daga kasashe 12 ( wato injiniyoyi 10  da ke da kwarewa ta fannin hada rahoto, sai kuma ‘yan jaridu 10) wadanda suka samu horo daga Rachel Locatelli, shugabar sashen bayar da horo ta RFI da Muriel Pomponne, ‘yar jarida a RFI kuma shugabar sashen labarai na harsunan kasashen ketare.

Wannan horo na tsawon makonni biyu, ya gudana ne a ofishin RFI mandenkan da kuma Fulfulde da ke birnin Dakar.

Bayan kammala horon ne aka bukaci ‘yan jaridar su hada rahoto mai taken « Tattaunawa da iya hakuri da juna» yayin da su kuma injiniyoyi suka gudanar da nasu aikin akan wasu ayyukan hannu a cikin kasar Senegal.

Wanda suka yi nasara

Alkalan da suka sanya ido game da gasar, sun bayyana gwarzayen bana da cewa su ne:

Esther SENPA BLAKSEMDI, mai shekaru 25, ‘yar asalin kasar Kamaru, wadda ta mallaki digiri daga makarantar koyon aikin jarida da yada labarai mallakin CRTV. yanzu haka tana aiki ne da CRTV.

Ta shirya rahoto a game da yara da ke fama da wata cuta mai kama fatar jiki. Alkalan gasar, sun yaba a game da wannan rahoto mai wuyar hadawa da kuma sarkakkiya.

Henintsoa Tiana Miranto RAKOTOMALALA, mai shekaeru 26, daga kasar Madagascar, ya mallaki digiri na biyu a game da kimiyar yada labarai wanda ya samu daga Makarantar horos da aikin jarida ta kasar.

Injiniya ne da ke aiki a Aceem Radio Madagascar. Rahotonsa « cikin komai akwai sauti » ya mayar da hankali ne game da bai wa masu saurare damar sanin aikin masu horos da kwallon kafa ga yara kanana.

Alkalan gasar sun yaba sosai da wannan rahoto saboda tsara shi musamman ingancin sautuka da kuma yadda ake gina labarin da ke cikinsa.

Wadannan rahotonni guda biyu, an wallafa su tun a ranar 2 ga watan Nuwamba a labaran karfe 7 da rabi na yamma da kuma alhamis 3 ga wata a labaran safe na Afirka.

Alkalan gasar

Kwamitin alkalancin gasar ya kunshiCécile Mégiewaccedaratkar RFI ce,a matsayin shugaba, Vincent Hugeux, babban mai hada rahoto kuma malami a sashen koyon aikin jarida da ke Sciences Po, da Stéphanie Rabourdin, mataimakiyar darakta a makarantar koyon aikin yada labarai ta (INA), Mamoudou Ibra Kane, wakilin ‘yan jarida daga Senegal, kuma shugaban kafar yada labarai ta Emedia, Frédérique Misslin, mataimakiyar daraktan RFI mai kula da labaran duniya, Charlotte Idrac, wakiliyar dindindin ta RFI a Dakar, Benjamin Avayou, mataimakin shugaban sashen samar da kayan aiki na RFI, Alassane Bireba, shugaban sashen injiniyoyi a RFI mandenkan da  fulfulde, sai Yves Rocle, mataimakin shugabar Daraktar RFI mai kula da harsunan Afirka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.