Isa ga babban shafi

Rasha na shan matsin lamba kan harin da aka kai Poland

Amurka da kawayenta sun soki Rasha a kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya wajen dora mata alhakin harin makami mai linzami da aka kai Poland, lamarin da babban jami'in siyasa na Majalisar Dinkin Duniya ya kira ayi taka tsan-tsan rurura wutan rikicin Ukraine na watanni tara.

Wani mutum ya daga tutar Ukraine da Poland yayin wata zanga-zanga a gaban wani gini dauke da jami'an diflomasiyyar Rasha a birnin Warsaw na kasar Poland, Lahadi, 13 ga Maris, 2022.
Wani mutum ya daga tutar Ukraine da Poland yayin wata zanga-zanga a gaban wani gini dauke da jami'an diflomasiyyar Rasha a birnin Warsaw na kasar Poland, Lahadi, 13 ga Maris, 2022. © Czarek Sokolowski / AP
Talla

Kungiyar Tsaro ta NATO wanda ta shirya taron gaggawa kwana daya bayan harin makami mai linzamin da ya kashe manoma biyu a Poland, ta bayyana shi a matsayin wani hari da dakarun tsaron sararin samaniyar Ukraine suka harba domin kariya daga hare-haren Rasha.

Lamarin na zuwa ne a ranar da Rasha ta harba makamai masu linzami sama da 90 a biranen Ukraine, da nufin tsanta matsalar makamashinta da kuma katse wutar lantarki ga miliyoyin mutane, wanda Kyiv ta ce shi ne tashin hankali mafi muni da suka gani tun bayan da Moscow ta mamaye Ukraine a ranar 24 ga watan Fabrairu.

Sa'ida

Zurfin Nazarin NATO da Poland da duk suka nesanta  Rasha da wannan hari, ya dan kwantar da hankalin  kasashen duniya dake fargabar abin da ka iya biyo bayan taba wata kasa dake mamba cikin kungiyar tsaro mafiya karfi a duniya.

Ko da yake shugaban Ukraine Volodymyr Zelenskyy ya ci gaba da dagewa babu tantama harin ba daga kasar sa bane.

Amurka

Jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya, Linda Thomas-Greenfield, ta shaidwa Kwamitin Sulhun cewar ko da kuwa kai tsaye ba Rasha bace ta kai harin, dole a daura mata alhaki saboda haramceccen yaki da ta kaddamar kan Ukraine.

Jakadun Majalisar Dinkin Duniya na Poland da Birtaniya sun yi na'am da bayanin cewa mamayewar Rasha ne a karshe ke da alhakin abin da ya faru a Poland.

Zargin Rasha

Jakadan Rasha na Majalisar Dinkin Duniya Vassily Nebenzia ya mayar da martani, inda ya zargi Ukraine da Poland da kokarin haifar da rikici kai tsaye tsakanin Rasha da NATO, kuma ya yi nuni da kalaman shugaban Ukraine da jami'an Poland da farko na nuna cewa Rasha ce ke da alhakin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.