Isa ga babban shafi

Ukraine ce ta kai hari Poland cikin kuskure

Kwararru sun ce, bisa dukkan alamu, Ukraine ce ta kaddamar da harin makami mai linzami kan kasar Poland cikin kuskure, amma ta danganta harin da Rasha.

L'explosion à Przewodow, un village polonais près de la frontière avec l'Ukraine.
L'explosion à Przewodow, un village polonais près de la frontière avec l'Ukraine. © via REUTERS
Talla

Shugabannin kasashen duniya da suka hada da na Amurka Joe Biden, sun yi taka-tsan-tsan wajen mayar da martani

Rasha dai ta musanta wannan zargin , yayin da kakakin gwamnatin kasar, Dmitry Peskov ke cewa,

Babu wani dalilin shiga zaman tankiya, ya kamata ku sani cewa, kassar Poland ta mallaki dukkanin fasaha da kwarewa , kuma tana da na’urar  kare kanta daga makamai mai linzami samfurin  S. 300. Sannan dukkanin kwararri sun tabbatar da cewaa, makamin da ake magana a kai, ba na sojojin Rasha ba ne.

 

Peskov ya kuma ce, ya kamata a daina cece-kuce, yana mai bukatar jama’a da su mayar da hankali kan martanin da ya fito daga Amurka biyo bayan wannan harin, wanda ya sha ban-ban da irin martanin da Poland ta mayar.

Kazalika gwamnatin Rasha ta gargadi mahukuntan Poland da su kiyaye lafuzzansu kan wannan batu mai cike da hatsari.

Yanzu haka gwamnatin Rasha ta kira jakadan Poland da ke kasarta biyo bayan zargin da aka yi mata na kaddamar da harkin wanda ya kashe fararen hula biyu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.