Isa ga babban shafi

Sabon shugaban Twitter zai kori ma'aikata a kamfaninsa na Afrika

Rahotanni sun ce, matakin Elon Musk sabon shugaban kamfanin Twitter, na korar dubban ma’aikata ya shafi sabuwar hedkwatar kamfanin ta nahiyar Afirka da ba a dade da kafawa ba.

Sabon mai kamfanin Twitter, , Elon Musk.
Sabon mai kamfanin Twitter, , Elon Musk. REUTERS - DADO RUVIC
Talla

Wasu ma'aikata a babban Ofishin kamfanin na Twitter a Afirka ne suka tabbatarwa manema labarai cewar korar da aka yi wa takwarorinsu a sassan duniya ta shafe su tun lokacin da Elon Musk ya kammala saye dandalin sada zumuntar na zamani.

A watan Afrilun shekarar 2021, Twitter ya kafa hedkwatarsa ta nahiyar Afirka a Accra, babban birnin kasar Ghana.

An dai kiyasta matakin Musk na kora, zai shafi jami’ai dubu 3,700, kusan rabin adadin ma’aikatan kamfanin nasa dake sassan duniya.

Tun cikin makon da ya gabata ne kuma, ma'aikata da  dama suka sanar da cewa an kulle shafukan da suke amfani da su wajen gudanar da ayyukansu.

Zalika ma’aiakatan da ke hedikwatar kamfanin Twitter na Afirka sun tabbatar da samun wasikun da ke shaida musu cewar, za a iya korarsu daga bakin aiki, kamar yadda lamarin ya auku ga sauran takwarorinsu a sassan duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.