Elon Musk ya sallami manyan jami'an kamfanin Twitter
Fitaccen attajirin duniya Elon Musk ya karbe iko da kamfanin sadarwar twitter akan Dala biliyan 44, yayin da nan take ya kori shugabannin gudanarwarsa.
Wallafawa ranar:
Wannan shine karo na farko da daya daga cikin manyan attajiran duniya ya karbe iko da kafofin sadarwar da jama’a ke aiki da su.
Yana karbe iko da kamfanin, attajiri Elon Musk ya wallafa cewar, ‘an yantar da tsintsuwar twitter‘, a wani shagube da yayi dake nuni ga alamar tsuntsun da kamfanin ke amfani da shi.
Nan take Musk ya sanar da korar shugaban kamfanin Parag Agrawal da shugaban sashen kudinsa da kuma shugaban bangaren kula da tsaftacce ayyukan kamfanin.
Shi dai Agrawal a baya ya ruga kotu inda ya nemi goyan bayan ta akan yarjejeniyar sayar da kamfanin, yayin da aka kammala cinikin tun kafin kotun ta yanke hukunci akan karar da ya shigar.
Tuni wannan ciniki ya haifar da martani daga sassa daban daban, ciki harda shugaban kula da hanyoyin sadarwar kasashen Turai, Thierry Breton wanda ya bukaci Musk ya mutunta dokokin hulda da jama’ar dake yankin, yayin da tsohon shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewar yanzu kamfanin twitter ya koma hannun masu hankali.
Trump yace yana matukar farin cikin cewar daga yanzu marasa hankali da kuma mahaukatan da suka tsani kasarsu ta Amurka ba zasu ci gaba da iko da kamfanin ba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu