Isa ga babban shafi

EU ta bukaci kafa kotun kasa da kasa kan yakin Ukraine

Tarayyar Turai ta yi kira da a kafa wata kotun musamman ta kasa da kasa da za ta saurari batutuwan da suka shafi laifukan yaki, biyo bayan gano manyan kaburbura a wani yanki na Ukraine.

wasu daga cikin daruruwan gawarwakin da aka tono a garin Iziyum da sojojin Ukraine suka kwato daga hannun Rasha.
wasu daga cikin daruruwan gawarwakin da aka tono a garin Iziyum da sojojin Ukraine suka kwato daga hannun Rasha. AP - Evgeniy Maloletka
Talla

Kiran ya biyo bayan gano manyan kaburbura da aka binne gawarwakin da yawansu ya kai kimanin 450 ne a yankin Iziyum da dakarun Ukraine suka kwato daga hannun Rasha, inda aka ga alamun azabtarwa a tattare da wasu daga cikin gawarwakin da aka tono.

Wani wakilin kamfanin dillancin labaran Faransa da yake wurin da aka tono wadannan gawarwaki ya ruwaito cewa ya ga wasu da aka daure hannuwansu ta baya.

A ranar Alhamis da ta gabata, shugabar kungiyar Tarayyar Turai, Ursula von der Leyen ta ce bukatarta ita ce ganin shugaba Vladimir Putin ya gurfana a gaban kotun hukunta manyan laifuka ta duniya a kan laifukan yaki.

Jagoran diflomasiyyar Tarayyar Turai Josep Borrell, wanda ya bayyana kaduwa sakamakon gano manyan kaburburan, ya bayyana abin da ya kira ‘halin rashin tausayi’ da dakarun Rasha ke nunawa a matsayin watsi da dokar jinkai ta kasa da kasa, kamar yadda aka tsaida a taron Geneva.

Ana nan dai ana ci gaba da gwabza yaki da aka fara a watan Fabrairu tsakanin Rasha da Ukraine, kuma kowane bangare na ikirarin nasara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.