Isa ga babban shafi

Rasha ta sanar da kashe sojin Ukraine 200 a hari kan tashar jiragen kasa

Ma’aikatar tsaron Rasha ta ce ta kashe sojojin Ukraine fiye 200 a harin da ta kai tashar jirgin kasan da ke tsakiyar kasar, harin da mahukuntan Kiev suka ce ya kashe mutane 25 ciki har da kananan yara.

Wani bangare na tashar jirgin kasan da Rasha ta farmaka a Ukraine.
Wani bangare na tashar jirgin kasan da Rasha ta farmaka a Ukraine. AP - Felipe Dana
Talla

Sanarwar da ma’aikatar tsaron ta Rasha ta fitar ta ce sakamakon harin da ta kai da makami mai linzami na Inkander kan jirgin kasan da ke dauke da sojojin Ukraine a tashar Chaplyne na yankin Dnipropetrovsk ta kashe Sojojin fiye da 200 tare da lalata manya-manyan kayakin yaki da suka kunshi makamai da motoci har guda 10.

Ma’aikatar ta ce tawagar sojojin na shirin kai farmakin daukar fansa ne kan dakarun Rasha da ke gabashin Donbas yankin da tuni ya fada hannun Rasha tun a watannin baya.

Tuni da kungiyar Tarayyar Turai da Amurka suka yi tir da harin wanda ke zuwa dai dai lokacin da Ukraine ke tsaka da bikin ranar ‘yanci da kuma cika watanni 6 da faro mamayar ta Rasha.

Ko watan Aprilu makamancin harin na Rasha kan tashar jiragen kasa ta Kramatorsk ya hallaka fararen hula 57.

Ukraine na amfani da tashoshin jiragen kasan ne a matsayin hanya mafi sauki don kara yawan dakarunta da ke fatattakar Sojin Rasha a hare-haren da kasar ke ci gaba da kaiwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.