Isa ga babban shafi

Za mu ci gaba da yaki har sai mun kawar da barazanar Rasha- Zelensky

Shugaba Volodymyr Zelensky ya ce Ukraine za ta ci gaba da yaki don kawo karshen mamayar Rasha ba tare da la’akari da irin karfin Sojin da makwabciyartata ke da shi ba.

Shugaba Volodymyr Zelensky na Ukraine yayin jawabin kai tsaye a birnin Kiev.
Shugaba Volodymyr Zelensky na Ukraine yayin jawabin kai tsaye a birnin Kiev. AP - Ludovic Marin
Talla

A jawabinsa na kai tsaye ga al’ummar kasar Zelensky ya ce Ukraine bazata mika wuya ga Rasha ba, ba kuma za ta bukaci tattaunawa don kawo karshen yakin ba.

Zelensky ya ci gaba da cewa al’ummar Ukraine basu da damu da irin yawan Sojojin da Rasha ke da sub a, haka zalika basu damu da karfin da kasar ke da shi, abin da suka damu da shi kadai shi ne kare martabar kasarsu da kuma kawo karshen mamayar Moscow.

Shugaban na Ukraine Volodomyr Zelensky da ke samun goyon bayan manyan kasashen Duniya ciki har da Amurka da Turai ya bayyana cewa idan aka yi la’akari da yadda Ukraine ta yaki mamayar Rasha cikin watanni 6 da suka shafe suna gwabza yaki hakan na nufin za su iya jure wani lokaci mai yawa a nan gab aba tare da neman sulhu ko mika wuya ba.

A cewarsa cikin kowacce rana da ke gushewa sukan kara samun dalilin ci gaba da kare kasarsu ba tare da karaya ba.

Zelensky cikin jawabin nasa ya ce ba gudu babu ja da baya game da kalubalantar ballewar Ukraine, domin kuwa baza su sallama ko da yanki guda daga yankuna 25 da kasar ke da su ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.