Hukumomin Girka sun kwashe mutane daga yankin Lesbos
A yankin Lesbos na kasar Girka, jam’ian kwana-kwana sun yi amfani da jirage 7 da wani jirgi mai saukar ungulu wajen kai dauki tare da kwashe jama’a na yankin da baki yan yawon bude ido da wutar daji ta ritsa da su a wannan tsibiri da ya sha’ara wajen karbar baki yan yawon bude ido.
Wallafawa ranar:
Hukumomin yankin sun bayyana cewa wutar ta tashi ne da misalin karfe 10 agogon kasar a yau asabar,rashin kyawon yanayi da iska su taimakawa wuta bazuwa zuwa wasu yankuna cikin dan kankanin lokaci.
Al’amarin da ya sa magajin garin yammacin Lesbos Taxiarchis Verros bada umurni kwashe mutanen yankin cikin gaggawa, ba tareda bada adadin mutanen da aka samu nasarar kwashewa daga wannan yankin ba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu