Isa ga babban shafi

Dukkanin ma'aikata 8 da ke jirgin saman Ukraine da ya fadi a Girka sun mutu

Dukkanni ma’aikata 8 dake cikin wani jirgin daukar kaya, mallakin kasar Ukraine da ya yi hatsari a Girka a kan hanyarsa ta zuwa kasar Bangladesh daga Serbia dauke da makamai na soji sun mutu, kamar yadda nministan tsaron Serbia ya bayyana a yau Lahadi.

Baraguzan jirgin daukar kirar Antonovda ya fadi a Girka.
Baraguzan jirgin daukar kirar Antonovda ya fadi a Girka. AP - Giannis Papanikos
Talla

Ganau sun ce sun ga lokacin da jirgin kirar Antonov ya kama da wuta, ya kuma yi bindiga sau da dama.

hotunan bidiyo da suka karade shafunan sada zumunta na zamani a yau lahadi sun nuno yadda wani curin wuta ya kama jirgin kafin ya rikito kasa a daren Asabar.

Ministan tsaron Serbia, Nebojsa Stefanovic ya shaida wa wani taron manema labarai cewa, abin takaici dukkannin ma’aikatan jirgin 8 sun mutu.

Ma’aikatar harkokin wajen Ukraine ta ce dukkanin ma’aikatan jirgin da suka mutu ‘yan kasarta ne, kuma lalacewar injinan jirgin ne ummul’aba’isin hadarin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.