Isa ga babban shafi

Wani jirgin dakon kaya ya kama da wuta tun daga sama a kasar Girka

Hukumar kashe gobarar Girka ta ce wani jirgin dakon kaya Antonov An-12 ya yi hatsari da yammacin ranar Asabar a kusa da Paleochori Kavalas da ke arewacin kasar.

Yadda wuta ke ciki a wurin da wani jirgin sama ya yi hadari, mai nisan mil kadan daga birnin Kavala, a arewacin kasar Girka, Asabar, 16 ga Yuli, 2022.
Yadda wuta ke ciki a wurin da wani jirgin sama ya yi hadari, mai nisan mil kadan daga birnin Kavala, a arewacin kasar Girka, Asabar, 16 ga Yuli, 2022. AP - Ilias Kotsireas
Talla

Shaidun gani da ido sun ce jirgin na cin wuta kuma sun ji karar fashewar abubuwa kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Athens ya ruwaito.

Jami'an kashe gobara

Jami’an yankin sun ce an tura motocin kashe gobara bakwai zuwa wurin da hatsarin ya faru amma ba za su iya isa ba saboda fashe-fashen da ke ci gaba da aukuwa a jirgin.

Rahotanni daga kafafen yada labarai sun ce jirgin dakon kaya ya taso ne daga Sabiya zuwa kasar Jordan, kuma ya bukaci a ba shi izinin yin saukar gaggawa a filin jirgin saman Kavala da ke kusa, amma bai samu isa tashar ba.

Tashar talabijin ta ERT ta gwamnati ta bayar da rahoton cewa, jirgin na kasar Ukraine ne, wanda a cewar mutanen kauyen tuni ya fara cin wuta kafin ya fado.

Adidin wadanda ke ciki

Kawo yanzu dai babu wani bayani a hukumance game da adadin mutanen da ke cikin jirgin da ke ci gaba da konewa kamar yadda faifan bidiyo da aka watsa kai tsaye a gidan talabijin na kasar suka nuna.

Sai dai ERT ta ruwaito cewa jirgin na dauke da mutane 8 kuma kayan da yake da su na da hadari. Rahoton ya kara da cewa ‘yan sanda sun bukaci ‘yan jarida da ke wurin da su sanya abin rufe fuska.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.