Isa ga babban shafi

Ingila na shagulgulan cikar Sarauniya Elizabeth shekaru 70 a kan mulki

Dubban mutane ne suka yi dandazo yau alhamis a tsakiyar birnin London don gudanar da shagulgulan taya Sarauniya Elizabeth murnar cika shekaru 70 akan karagar mulkin Ingila, a wani gagarimin shagali da ake ganin ya iya zama na karshe a tsawon lokacin da ta dauka ta na mulki.

Dafifin jama'a a gab da fadar Buchingham.
Dafifin jama'a a gab da fadar Buchingham. AP - Alberto Pezzali
Talla

Tuni aka fara mabanbantan faretin ban girma ga Sarauniyar mai shekaru 96 wadda ake sa ran za fito bainar jama’a har sau biyu yayin shagulgulan a gab da fadar Buckingham.

Tun da sanyin safiya, daruruwan jama’a daga sassan Birtaniya da kuma wasu daga wajen kasar suka rika dafifi tare da tattaruwa a gab da fadar ta Buchingham galibinsu dauke da furannin girmamawa.

A watannin baya-bayan nan ne aka fara jita-jitar yiwuwar gudanar da kasaitaccen biking a Sarauniya Elizabeth duk da yadda Basarakiyar ta takaita shiga cikin jama’a tun a bara saboda wahalar da yawan zama da tashi ke bata da kuma tsoron cutar Covid-19.

Sarauniya Elizabeth ita ce mafi dadewa akan karagar mulkin Ingila bayan gado daga hannun mahaifinta sarki George na 6.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.