Isa ga babban shafi
Birtaniya - Korona

Sarauniyar Ingila Elizabeth ta II ta harbu da annobar korona

Firayim Ministan Burtaniya Boris Johnson ya yi wa Sarauniya Elizabeth ta II fatan samun sauki cikin sauri bayan da gwaji ya tabbatar  da basarakiyar mai shekaru 95 ta harbu da annobar korona, kwana biyu bayan bukin cikarta shekaru 70 akan karagar mulki.

Sarauniyar Inglia Elizabeth II ta harbu da korona, 20/02/2022.
Sarauniyar Inglia Elizabeth II ta harbu da korona, 20/02/2022. CHRIS JACKSON BUCKINGHAM PALACE/AFP/File
Talla

Mista Johnson wanda ya wallafa sakon ta shafinsa na Twitta ya bukaci ‘yan kasar da ma sauran al’umma da su yiwa Sarauniyar fatan samun lafiya cikin sauri.

Labarin na zuwa ne a wani mawuyacin lokaci na abin kunya ga dangin masarautar kuma bayan Yarima Charles, babban ɗan sarauniya kuma magaji, shima  ya harbu da cutar  a ranar 10 ga watan Fabrairu, kwana biyu bayan ganawa da mahaifiyarsa a Windsor Castle.

Babu wani bayani da aka bayar kan ko Sarauniya Elizabeth ta yi wani gwajin Covid da kanta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.