Isa ga babban shafi
Birtaniya

Fadar Sarauniyar Ingila na yi min karya- Markle

Uwargidan Yarima Harry, jikan Sarauniya Elizabeth ta Biyu, Meghan Markle ta bayyana cewar fadar Buckingham na yada labaran karya a kanta da kuma mijinta domin bata musu suna, a wata hira da ta yi da fitacciyar mai shirin talabijin din Amurka Oprah Winfrey.

Meghan Markle da mijinta Yarima Harry.
Meghan Markle da mijinta Yarima Harry. Daniel Leal-Olivas AFP/Archivos
Talla

Wadannan kalamai masu zafi na daga cikin batutuwan da ke nuna tsamin dangantaka tsakanin iyalan gidan sarautar Birtaniya da kuma Yarima Harry da uwargidansa da suka koma zama a Amurka.

Wani sashe na hirar da aka yada na zuwa ne bayan da fadar Buckingham ta sanar da kaddamar da bincike akan Markle cewar ta ci zarafin wata ma’aikaciyar fadar watanni bayan auranta da dan gidan Sarautar.

A shekarar da ta gabata, Harry da uwargidansa Markle sun bayyana shirinsu na janyewa daga gudanar da harkokin da suka shafi gidan sarautar matakin da ya  nuna tsamin dangantakar da ke gudana a gidan.

Fitar da iyalan daga harkokin mulkin gidan sarautar ya tabbata a farkon wannan shekarar, yayin da fadar sarauniyar da na Yarima Harry ke kokarin bayyana abin da ya faru da zummar neman goyan bayan jama’a.

A ranar Lahadi mai zuwa ake saran Winfrey Oprah ta watsa cikakkiyar hirar a Amurka, yayin da mazauna Birtaniya kuma za su kalle ta a ranar Litinin.

A wata hirar da aka yada a farkon wannan mako, Yarima Harry ya bayyana fargabarsa ta ganin tarihi ya sake maimaita kansa, lokacin da yake nuni da abin da ya shafi mutuwar mahaifiyarsa Diana.

Ita dai Diana ta mutu ne sakamakon hadarin mota a Paris lokacin da masu dukar hoto ke bin ta da gudu.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.