Isa ga babban shafi

Kotun Faransa ta samu kamfanin Lafarge da laifin taimakawa ta'addanci a Syria

Kotun daukaka kara a Faransa ta tabbatar da tuhumar da ake kan kamfanin siminti na Lafarge wanda tun a shekarar 2019 kotu ta same shi da laifin taimakawa ayyukan ta’addanci a Syria baya ga aikata laifukan take hakkin dan adam, amma kuma ya yi nasara gaban kotu gabanin daukaka kara.

Shalkwatar kamfanin siminti na Lafarge-Holcim a birnin Paris.
Shalkwatar kamfanin siminti na Lafarge-Holcim a birnin Paris. © AFP/Franck Fife
Talla

Zaman kotun na jiya laraba ya tabbatar da hannun Lafarge wajen taimakon kungiyar ta’addanci ta IS da sauran kananun kungiyoyi masu ikirarin jihadi da suka taka rawa yayin yakin basasar Syria, matakin da ke bada tabbacin yiwuwar kamfanin ya fuskanci babbar shari’a don yi masa hukunci kana bin da ya aikata.

Kungiyoyin kare hakkin dan adam da suka yi tsayin daka wajen ganin an hukunta Lafarge na son shari’ar ta zama darasi ga sauran manyan kamfanonin da ke kawar da kai ga ta’addancin kungiyoyi matukar za sus amu zarafin ci gaba da gudanar da hada-hadarsu a yankin da ake samun tashe-tashen hankula.

Kamfanin na Lafarge da yanzu ke karkashin katafaren kamfanin gine-gine na Switzerland wato Holcim bayanai sun ce ya biya IS kudin ya yawansa ya kai yuro miliyan 13 tsakanin shekarar 2013 zuwa 2014 don bashi damar ci gaba da harkokinsa a yankin da mayakan kungiyar ta’addancin ke da tasiri.

A shekarar 2019 kamfanin ya musanta zarge-zargen da ake masa na biyan IS da sauran kananun kungiyoyin ta’addancin kudi baya ga taimakawa wajen take hakkin dan adam inda ya yi nasara gaban kotu gabanin daukaka kara.

Hukuncin na jiya laraba na nuni da cewa kamfanin da manyan jami’ansa 8 za su gurfana gaban kotu ciki har da tsohon shugabansa Bruno Lafont wanda a lokacinsa ne badakalar ta faru.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.