Isa ga babban shafi
Faransa-Syria

Lafarge zai fuskanci sabuwar tuhuma kan taimakawa ta'addanci a Syria

Babbar kotun Faransa ta yi watsi da hukuncin da wata karamar kotu ta yanke a baya, da ke jingine zarge-zargen da ake yi wa kamfanin siminti na Lafarge kan cewa ya taimaka wa kungiyoyin ta’addanci a Syria don aikata laifufukan da suka shafi cin zarafin bil’adama.

Katafaren kamfanin siminti na Lafarge.
Katafaren kamfanin siminti na Lafarge. © Captura de pantalla/Europe 1
Talla

Hukuncin wanda babbar kotun ta yanke a wannan talata, na matsayin gagarumin koma-baya ga kokarin da kamfanin simintin na Lafarge ke yi don wanke kansa daga zarge-zargen taimaka wa ayyukan masu da’awar jihadi da milyoyin kudade a kasar ta Syria.

An dai gurfanar da kamfanin gaban kotu ne bisa zargin cewa ya kulla wata yarjejeniya a asirce da kungiyoyin ‘yan ta’adda domin ba shi damar ci gaba da gudanar da ayyukansa a cikin Syria a daidai lokacin da kamfanoni da dama suka dakatar da ayyukansu saboda da tsanantar yaki a kasar.

Sabon hukuncin dai ya bukaci a sake gudanar da bincike dangane da illahirin zarge-zargen da ake yi wa kamfanin na Lafarge, tare da bayar da damar gabatar da sabon zargi da ya shafi jefa ‘’rayukan ma’aikatansa cikin hadari’’.

Idan aka tabbatar da cewa Lafarge ya taimaka wa ta’addanci, hakan na nufin cewa kamfanin ya aikata babban laifi sannan kuma ya karya takunkuman da kungiyar Turai ta shimfida da ke haramta zuba jari a Syria tsakanin 2013 zuwa 2014.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.