Isa ga babban shafi

Mune muka kai hari a Kyiv yayin da sakataren MDD ke ziyara a birnin - Rasha

Rundunar sojin Rasha ta tabbatar da cewar ita ce ta kai wani hari ta sama kan birnin Kyiv a kusa da inda sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya ya kai ziyara.

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya António Guterres yayin ziyarar da ya kai zuwa garin Borodianka da ke kusa da birnin Kyiv.
Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya António Guterres yayin ziyarar da ya kai zuwa garin Borodianka da ke kusa da birnin Kyiv. © Reuters/Gleb Garanich
Talla

Ma'aikatar tsaron Rasha ta ce ta yi amfani da makamai masu linzamin da ke cin dogon zango wajen kai hari a birnin Kyiv ne domin lalata gine-ginen kera makamai na Artyom da ke babban birnin.

Harin dai shi ne na farko da Rasha ta kai a babban birnin kasar ta Ukraine cikin kusan makwanni biyu, inda wata ‘yar jarida ta mutu, bayan da makami mai linzami ya fada kan ginin da take ciki.

Tuni dai shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya yi kira ga kasashen duniya da su mayar da martani mai karfi kan hare-haren na ranar Alhamis da Rasha ta kai, a daidai lokacin da babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ke ziyara a kasar, abinda ya bayyana a matsayin tsokana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.