Isa ga babban shafi
Belgium-Turai

'Yan sandan Belgium sun kame gomman masu safarar kwayoyi a Turai

Masu gabatar da kara a Belgium sun sanar da nasarar kame gomman mutane a wani samame da ‘yan sandan kasar suka kai da taimakon ‘yan sandan Tarayyar Turai a kasashe nahiyar 6 na kan masu fataucin miyagun kwayoyi na kasa da kasa.

Ko a 2020 mutane 30 aka kame a Belgium da ke safarar miyagun kwayoyi.
Ko a 2020 mutane 30 aka kame a Belgium da ke safarar miyagun kwayoyi. AFP/File
Talla

Mutane 30 ne aka kama a Belgium, inda aka kaddamar da binciken a shekarar 2020, da kuma wasu ‘yan daidaiku da aka kama a kasashen ketare, a cewar wata sanarwa daga ofishin babban mai gabatar da kara na Belgium, wadda ta ce an gudanar da jerin bincike har 109 a kasashen Jamus, Italiya, Spain, Netherlands da Croatia.

Gungun  masu safarar muggan kwayoyin da aka kai wa samamen sun shahara ne a harkar dillancin hodar ibilis daga Kudancin Amurka, kuma sun samu damar gudanar da bincike a kansu ne da taimakon wani kuste da aka wa wata wayarsu ta tafe- da- gidanka da suke amfani da ita a kungiyance.

Batun na baya bayan nan dai ya shafi wasu masu safarar muggan kwayoyi ne daga gabashinTurai da ke zaune a yankunan birnin Brussels da kuma wasu ‘yan kudancin Turai da ke kungiyar mafiar nan ta Limburg, wato wani lardi da ke iyaka da Netherlands da suka yi kaurin suna wajen samar da muggan kwayoyi.

Wannan kame dai na zuwa ne bayan da a farkon wannan wata wani babban alkali, Ignacio de la Serna ya yi kashedin cewa yanzu fa ‘yan sanda ba su da nasibin dakile barazanar masu safarar mugga kwayoyi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.