Isa ga babban shafi
Paris-Zanga-zanga

'Yan sandan Paris sun kama mutane 81 kan adawa da rigakafin Korona

‘Yan sanda a Faransa, sun kama mutane 97 da suka karya dokar da ta hana zanga-zangar kin amincewa da ka'idojin coronavirus tare da hana zirga-zirga a birnin Paris, yayin da 81 har yanzu ke tsare.

'Yan sandan kwantar da tarzoma a wajen zanga-zangar Paris.
'Yan sandan kwantar da tarzoma a wajen zanga-zangar Paris. REUTERS - BENOIT TESSIER
Talla

A birnin Paris, sama da motoci 100 ne suka yi cincirindo a kan titin Champs-Elysees, inda 'yan sanda suka yi amfani da hayaki mai sa hawaye wajen tarwatsa masu zanga-zangar.Masu gabatar da kara sun ce daya daga cikin wadanda ake tsare da su shine Jerome Rodrigues, shugaban kungiyar masu zanga-zangar, wanda ya yi ta fafatawa da 'yan sanda a kowane karshen mako na tsawon watanni da dama a karshen shekarar 2018 da farkon 2019.

 

Rundunar ‘yan sandan birnin Paris ta kuma ce an bude wani bincike na cikin gida bayan wani faifan bidiyo da ya bayyana a shafukan sada zumunta da ke nuna wani jami’in dan sanda ke nuna bindigarsa a kan wani direba.

Sama da motoci 400 ne suka yi sansani a wurare da dama da ke kusa da birnin Paris cikin dare, kuma masu shirya zanga-zangar sun yi kira ga mutane da su nufi Brussels don wata babbar zanga-zanga a yau Litinin, kamar yadda majiyar ‘yan sandan kasar ta Faransa ta tabbatar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.