Isa ga babban shafi
Faransa

Masu bore sun hana shugaban Faransa tattaki a Paris

An diga ayar tambaya kan tsarin bai wa shugaban Faransa Emmanuel Macron tsaro bayan wasu masu zanga-zanga sun tunkare shi kai-tsaye a yayin da yake tattaki tare da matarsa a wani lambu da ke birnin Paris.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron tare da matarsa Brigitte
Shugaban Faransa Emmanuel Macron tare da matarsa Brigitte Ludovic Marin / AFP
Talla

Masu zanga-zangar sanye da riguna launin rawaya sun yi ta furta munanan kalamai ga shugaba Macron duk da cewa yana tare da dogaransa a dandalin Tuileries da ke birnin Paris a jiya Talata.

Wani hoton bidiyo da aka wallafa a shafukan sada zumunta ya nuna yadda masu zanga-zangar ke yi wa shugaban ihu, suna masu fadin cewa, “ Macron demission” ma’ana Macron ka yi murabus, yayin da masu boren suka yi wa tawagar shugaban kuri.

Ala tilas dai, shugaban na Faransa ya tanka masu zanga-zangar da suka yi ta nuna masa yatsa a fuska tare da yi masa korafi kan rashin daidaito a bangaren tattalin arziki da kuma yadda jami’an ‘yan sanda ke amfani da karfi kan masu bore.

An dai jiyo shugaban na Faransa na mayar musu da martani kai-tsaye, yana mai cewa, “ ku sassauta” yayin da ya kasa kunne yana sauraren korafinsu.

Shugaban ya ce musu lallai ya fahimci kuncin da suke ciki, duk da dai ya ce, akwai masu tayar da hargitsi a tsakaninsu, lamarin da ya sa ‘yan sanda ke nuna musu karfi.

Babu dai wanda ya sanya kyallen rufe fuska tsakanin Macron da masu zanga-zangar a yayin musayar kalamai tsakanin bangarorin biyu.

A bangare guda, jagoran jam’iyyar masu tsattsauran ra’ayi a Faransa, Jean-Luc Melenchon ya ce, ya kamata Macron ya yi taka-tsan-tsan a matsayinsa na shugaban kasa wajen gudanar da irin wannan tattaki a yankin da ya-ku-bayi ke da rinjaye.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.