Isa ga babban shafi
Faransa

Tsohuwar ministar shari’ar Faransa na nazari kan takarar shugaban kasa

Tsohuwar ministar shari’ar Faransa, kuma jigo a bangaren masu sassaucin ra’ayi, Christiane Taubira, ta ce tana nazari a kan tsayawa takarar shugaban kasa a zabe mai zuwa, inda ta ce za ta sanar da hukuncin da ta yanke a cikin wata mai kamawa.

Tsohuwar ministar shari’ar Faransa, kuma jigo a bangaren masu sassaucin ra’ayi, Christiane Taubira.
Tsohuwar ministar shari’ar Faransa, kuma jigo a bangaren masu sassaucin ra’ayi, Christiane Taubira. AP - Kamil Zihnioglu
Talla

A wani faifen bidiyo da aka wallafa a dandalin sada zumunta, Taubira ta sha alwashin dinke barakar da ke tsakanin masu sassaucin ra’ayi.

Magoya bayan tsohuwar ministar shari’ar dai sun shafe watanni suna ta kira da ta fito takara don kasancewa shugaban Faransa bakar fata ta farko, da zummar dakile habakar da masu zazzafan ra’ayi ke yi.

A shekarar 2013 ne dai Taubira ta gabatar da batun auren jinsi, lamarin da ya janyo zanga- zanga da mahawara a majalisar dokokin Faransa, a lokacin da take matsayin ministar shari’a, a karkashin mulkin tsohon shugaba François Hollande.

Tsohuwar ministar shari’ar Faransa, kuma jigo a bangaren masu sassaucin ra’ayi, Christiane Taubira,
Tsohuwar ministar shari’ar Faransa, kuma jigo a bangaren masu sassaucin ra’ayi, Christiane Taubira, AFP - JEWEL SAMAD

Ta kuma yi fice a matsayin wadda ta jagoranci bukatar bijiro da dokar nan da ta ayyana cinikin bayi a matsayin laifin cin zarafin dan Adam a shekarar 2001.

Taubira, ta fito ne daga yankin Cayenne na jihar Guiana ta Faransa, kuma ta samu yabo daga masu sassaucin ra’ayi saboda kwarjininta a majalisar dokoki, da mahawarar da take yi a talabijin.

Ta tsaya takarar shugabancin Faransa shekaru 20 da suka wuce, inda ta samu nasarar lashe kaso 2 na kuri’un da aka kada a zagaye na farko a zaben.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.