Isa ga babban shafi
Faransa-Zaben Faransa

Mai ra'ayin rikau na neman shugabancin Faransa

Fitaccen mai fashin-baki a kafafen yada labaran Faransa kuma mai ra’ayin rikau, Eric Zemmour ya sanar da kudirinsa na tsayawa takara a zaben shugabancin kasar mai zuwa.

Ana yi wa Eric Zemmour lakabi da Trump na Faransa
Ana yi wa Eric Zemmour lakabi da Trump na Faransa BERTRAND GUAY POOL/AFP/File
Talla

Zemmour ya yi fice saboda kiyayyarsa ga baki, yayin da ake yi masa kallon mai tsananin nuna wariya da ba ya nuna nadama, amma duk da haka yana samun goyon baya musamman daga Faransawan da ke  ganin yana kare musu tsantsar al’adarsu.

Kuri’un jin ra’ayin jama’a da aka gudanar a watannin da suka shude sun nuna cewa, farin jinin Zemmour ya karu, amma alamu na baya-bayan nan na nuna cewa, karbuwarsa ta fara raguwa.

A wani sakon bidiyo da aka wallafa a shafin YouTube, Zemmour ya ce, ya kudirci daukar makomar kasar a hannunsa, yana mai alkawarin maido da martabar kasar a idon duniya.

Mai tsattsauran ra’ayin ya kara da cewa, yanzu ba lokaci ba ne na samar da sauyi a Faransa, ammam lokaci ne na ceto kasar.

Ana dai kallon kalamansa a matsayin kakkausan gargadi ga bakin da ke shiga cikin kasar ta Faransa.

Tuni wasu daga cikin Faransawa suka fara yi masa lakabi da “Trump na Faransa”, inda kuma ya yi amanna cewa zai kawar da shugaba Macron daga kujerasa saboda kudi da kuma goyon bayan da yake samu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.