Isa ga babban shafi
Faransa-Zaben Faransa

Watakila Macron ya kafa sabuwar jam'iyya kafin zaben badi

Wasu jiga-jigan abokanan siyasar shugaban Faransa Emmanuel Macron sun bukaci ya samar da wata sabuwar jam’iyya gabanin babban zaben kasar na shekara mai zuwa a wani yunkuri na ganin ya kai labari bayan gazawar jam’iyyar shugaban ta yanzu.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron
Shugaban Faransa Emmanuel Macron Ludovic MARIN AFP
Talla

Kalaman Ministan Tattalin Arzikin Faransa, Bruno Le Maire sun gasgata jita-jitar da ake da ita na yiwuwar Emmanuel Macron ya iya sauya sheka gabanin zaben na shekarar 2022 musamman bayan zaben baya-bayan nan da ya gano raunin da jam’iyyar shugaban ta LREM ke da shi a matakin yankuna da shiyyoyi.

Cikin kalaman Le Maire da ke matsayin babban jigo a gwamnatin shugaban, yayin wata hira da shi ta gidan talabijin na BFM ya nuna cewa, yana goyon bayan samar da wata kakkarfar jam’iyya da za ta goyi bayan Macron dari bisa dari gabanin babban zaben na badi.

Ko a zaben 2017 shugaba Macron mai shekaru 43 da kansa ya samar da jam’iyyarsa ta Republic on the Move, cikin watan Aprilun 2016 shekara guda gabanin zaben kasar, kuma ya yi nasarar kai labari.

Ko da yake har yanzu shugaba Macron na da farin jini ga Faransawa, jam’iyyarsa ta rasa kwarjini duk kuwa da kokarin cika alkawuran da ya dauka da ma dora tarin mata a madafun iko da kuma shigar da sabbin fuskoki cikin tafiyar.

Tun a Lahadin da ta gabata Stephane Sejourne, babban mashawarcin Macron kan siyasa ya fara kiran ganin shugaban ya kafa sabuwar jam’iyya, yayin da shawarar ta samu goyon bayan Francois Bayrou kwararre a harkokin siyasa kuma na hannun daman Macron.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.