Isa ga babban shafi
Faransa

Magajin garin birnin Paris ta shiga takarar neman shugabancin Faransa

Magajin Garin birnin Paris Anne Hidalgo ta yi shelar shiga takarar neman shugabancin kasar Faransa za zaben da ke tafe a shekarar 2022.

Magajin Garin birnin Paris Anne Hidalgo.
Magajin Garin birnin Paris Anne Hidalgo. AFP - THOMAS SAMSON
Talla

Hidalgo ta bayyana aniyar ta ce a birnin Rouen, sanarwar da ta kawo karshen hasashen watanni kan cewa za ta nemi jam’iyyar Socialist ta bata damar tsaya mata takara.

Fitacciyar ‘yar siyasar mai shekaru 62, da ta sake lashe zabe karo na 2 a matsayin magajin garin Paris a shekarar da ta gabata, ta samu yabo daga bangarori da dama kan tsarin gudanar da ayyukan ta a babban birnin Faransa.

A lokacin shugabancin Anne Hidalgo al’amura daban daban sun dauki hankalin duniya a birnin Paris, da suka hada da jerin hare-haren ta'addanci a shekarar 2015, zanga-zangar adawa da gwamnati ta Yellow Vest, mummunar gobarar da ta kone dadaddiyar mujami’ar Notre-Dame, barkewar annobar Korona, sai kuma nasarar da birnin na Paris ya samu dangane da karbar bakuncin wasannin gasar Olympics a 2024.

Har yanzu dai shugaba mai ci Emmanuel Macron bai bayyana aniyarsa ta sake tsayawa takara ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.