Isa ga babban shafi

Gwamnatin Faransa na shirin rufe wani masallaci tsawon watanni 6

Gwamnatin Faransa ta sanar da shirin rufe wani masallaci a kasar na tsawon watanni 6 saboda gabatar da wa’azi mai  cin karo da dokokin Kasar.

Babban masallacin birnin Paris
Babban masallacin birnin Paris parisinfo.com
Talla

Ministan cikin gidan Faransa Gerald Darmanin da yayi sanarwar, ya shaidawa gidan talabijin Cnews cewar yayi duk mai yiwuwa wajen tabbatar da rufe masallacin dake garin Bove a yankin WAZ mai nisan kilomita 100 daga arewacin birnin Paris, saboda yadda suke wa’azi ba bisa ka’ida ba.

Babban masallacin birnin Paris
Babban masallacin birnin Paris parisinfo.com

Ministan ya ce limamin masallacin na amfani da wa’azin shi ne wajen caccakar kristoci, masu auren jinsi daya da kuma yahudawa.

Tun da fari dai ne Hukumomin yankin WAZ suka bayyana aniyarsu ta rufe masallacin saboda irin wa’azin da ake gabatarwa a ciki, wanda ke sukan ra’ayi, ko haddasa rikici.

Masallaci
Masallaci © Reuters

Ita kuwa Jaridar courrier picard ta Kasar da tayi tsokaci kan batun, ta ce limamin masallacin mai gabatar da wa’azin sabon shiga ne a addinin musulunci kuma tuni hukumomin wannan yanki suka dakatar da shi daga aikin masallacin.

 

Tun a farkon shekarar 2020 ne Darmanin ya sanar da cewar faransa zata matsa kaimi wajen kula da yadda ake tafiyar da ayyukan mujami’u da ma kungiyoyi da ake zargi da yada kalaman batanci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.