Isa ga babban shafi
Sweden

Zababbiyar Firaministar Sweden ta yi murabus sa'o'i bayan an nada ta

Zababbiyar Firaministan Sweden Magdalena Andersson ta yi murabus daga mukamin nata bayan ‘yan sa’o’i da nada ta da majalisar dokokin kasar ta yi.  

Finance Minister Magdalena Andersson looks set to become Sweden's first woman prime minister
Finance Minister Magdalena Andersson looks set to become Sweden's first woman prime minister Jonathan NACKSTRAND AFP/File
Talla

Murabus din nata na zuwa ne bayan da kasafin kudin da ta gabatar  ya gaza samun shiga, gami da janyewar jam’iyya mai rajin kare muhalli daga hadakar da suka yi.

Anderson ta shaida wa manema labarai cewa, tsarin mulkin kasar ya tanadi cewa abu mafi dacewa shine duk wata gwamnatin hadaka ta yi murabus a duk lokacin da abokiyar hadakarta ta janye, tana mai cewa ba  za ta so ta jagoranci gwamnatin da za a  yi tababar halaccinta ba.

Ta ce tana fata a sake zabenta nan ba da jimawa ba a matsayin shugabar gwamnati mara rinjaye da ta kunshi jam’iyyar Social Democrats ne kawai.

A cikin wani yanayi mai cike da rudani, Andersson ta zama mace ta farko da aka zaba kan mukamin firaminista a kasar Sweden bayan da ta kulla yarjejeniyar karshe da jam'iyyar mai sassaucin ra’ayi ta wajen kara kudaden fansho don samun goyon bayanta a zaben na ranar Laraba.

Amma sai daya jam’iyyar ta masu rajin kare muhalli ta janye goyon bayanta ga kasafin kudin da Andersson ta gabatar, saboda yadda ta amince da kudirin masu sassaucin ra’ayi, lamarin da ya hana kasafin da ta gabatar samun shiga sakamakon karancin kuri’u.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.