Isa ga babban shafi
SWEDEN

Masu zazzafen ra'ayi na iya yin tasiri a zaben Sweden

A wannan lahadi ana gudanar da zaben ‘yan majalisar dokoki a kasar Sweden, a cikin wani yanayi da ake fargabar cewa masu zazzafan ra’ayi da kuma kyamar baki ne za su yi nasara.

Masu kada kuri'u a zaben kasar Sweden ranar 9 ga watan satumbar 2018
Masu kada kuri'u a zaben kasar Sweden ranar 9 ga watan satumbar 2018 REUTERS/Ints Kalnins
Talla

Kimanin mutane milyan 7 ne suka cancanci kada kuri’unsu a zaben na yau, inda rahotanni ke cewa an samu fitowar jama’a masu tarin yawa tun da sanyin safiyar yau.

Kwanaki biyu kafain zaben, shugaban jam’iyyar masu ra’ayin rikau Jimmie Åkesson ya gabatar da jawabi wanda a cikinsa ya furta wasu kalamai da ake fassarawa a matsayin kyama ga baki da ke rayuwa a kasar da kuma wadanda ke neman shiga kasar.

Sweden dai na daya daga cikin kasashen da suke karbar baki masu tarin yawa a yankin Turai, to sai dai masu adawa da kwararar bakin sun gudanar da yakin neman zaben su ne a kan wannan batu, yayin da wasu suka yi alkawarin daukar mataki a kan batun matukar dai suka yi nasara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.