Sweden za ta kori ‘Yan ci-rani
Hukumomin Sweden na shirin korar ‘Yan ci-rani kusan 80,000 wadanda suka shiga kasar a bara kuma ba tare da samun takardun izinin zama a kasar ba.
Wallafawa ranar:
Ministan Harkokin cikin gidan kasar Anders Ygeman yace zasu mayar da ‘Yan ci ranin a kasashensu a cikin shekaru masu zuwa.
Ministan yace an umarci ‘yan sanda da sauran jamian tsaro su tsara yadda za a mayar da bakin zuwa kasashensu.
Sama da mutane dubu dari da sittin suka nemi mafaka a Sweden a 2015, amma yanzu kasar ta dauki tsauraran matakai akan iyakokinta domin rage kwararsu.
Sama da ‘Yan ci-rani da Yan gudun hijira miliyan guda suka tsallaka zuwa Turai a bara yawancinsu ‘Yan Syria da Iraqi da Afghanistan da ke kauracewa yaki a kasashensu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu