Isa ga babban shafi
Ecuador

Fursunoni 68 sun mutu sakamakon tarzoma a gidan yarin Ecuador

Fursunonin da suka tayar da tarzomar da ta yi sanadin mutuwar akalla mutane 68 a wani gidan yari da ke Ecuador na sake kai wa juna hari, kamar yadda kakakin shugaban kasar ya fada a Asabar.

'Jami'an tsaro a gidan yarin Ecuador da aka yi tarzoma.
'Jami'an tsaro a gidan yarin Ecuador da aka yi tarzoma. AP - Jose Sanchez
Talla

Carlos Jijon ya ce kawo yanzu ‘yan sanda na kokarin shawo kan al’amarin bayan an kwashe sa’o’i ana gwabza fada tsakanin da wasun su ke dauke da bindigogi da ababen fashewa da kuma adduna.

Ya ce fursunoni daga wasu bangarori biyu na gidan yarin na kai wa juna hari  a wani sabon tashin hankali, wanda ya bayyana a matsayin mafi muni da aka taba samu.

Shugaba Guillermo Lasso ne ke sa ido kan kwamitin rikicin, ya kuma yi kira ga kungiyoyin fararen hula da su yi kokarin kulla hulda da fursunoni da kuma kawo karshen zubar da jini.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.