Isa ga babban shafi
ECUADOR

An baza dubban jami'an tsaro a Ecuador bayan mutuwar fursunoni 118

Ecuador ta tura 'yan sanda da sojoji kimanin 3,600 don tabbatar da tsaron gidajen yarinta yayin da dangin wadanda aka kashe a daya daga cikin fitattun gidan yarin kasar dake Kudancin Amurka ke neman bayanai game da makusantarsu.

Jami'an tsaron kasar Ecuador, 30 ga watan Satunbar 2021.
Jami'an tsaron kasar Ecuador, 30 ga watan Satunbar 2021. AFP - FERNANDO MENDEZ
Talla

Akalla fursunoni 118 aka kashe, shida daga cikinsu kuwa an fille kawunansu, yayin da wasu gungun kungiyoyi biyu masu adawa da juna dauke da bindigogi da gurneti suka shiga yaki a gidan yarin Guayaquil ranar Talata.

Yayin da yanzu haka wasu mutane 86 da suka jikkata sakamakon artuban ke karban magani.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.