Isa ga babban shafi
Ecuador

Fursunoni 62 sun mutu a wani rikicin gidan yari a Ecuador

Akalla Fursunoni 62 suka mutu sakamakon wani tashin hankalin da aka samu a gidajen yarin Ecuador, Yarin da suka fuskanci tashe-tashen hankulan rahotanni sun ce su ne mafi girma da kasar ke da su kuma su ke dauke da kaso mai yawa na mutanen da ke tsare.

Tuni dai aka shawo kan rikicin yayinda wadanda suka jikkata ake kula da lafiyarsu.
Tuni dai aka shawo kan rikicin yayinda wadanda suka jikkata ake kula da lafiyarsu. ®REUTERS/Nelson Rios
Talla

Rundunar 'yan Sandar kasar ta ce mutanen da suka mutu na iya zarce 62 a rikicin da ya mamaye gidan yarin da ke yankin Guayas, Azuay da Cotopaxi.

Shugaban kasa Lenin Moreno ya danganta rikicin da ayyukan kungiyoyin masu aikata laifuffuka wadanda suka haifar da tashin hankali a gidajen yari da dama.

Kwamandan 'yan Sanda Patricio Carrillo ya ce an samu tashin hankali a gidajen yari da yawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.