Isa ga babban shafi
Google-EU

Kamfanin Google ya yi rashin nasara gaban kotu a rikicinsa da EU

Kamfanin Google ya sake rashin nasara kan karar da ya daukaka game da tarar da kungiyar tarayyar turai ta sanya masa ta tsabar kudi yuro biliyan 2 da miliyan 400 dangane da samunsa da laifin cin amana wajen yi mata kutse a manhajar bincike bada sani ba.

Tambarin kamfanin google na Amurka.
Tambarin kamfanin google na Amurka. Tobias SCHWARZ AFP/Archivos
Talla

Kamfanin na Google da kungiyar ta turai sun faro rikicin kan zargin karya ka’idar aminci tsakaninsu ne tun daga shekarar 2017 inda tun a wancan lokaci kotun EU ta ci tarar kamfanin yuro biliyan 2 da miliyan 400 amma kuma kamfanin na Amurka ya daukaka kara.

Sai dai a hukuncin da kotun Lexembourg ta zartas kan daukaka karar ta Google ta tabbatar da hukuncin da kotun ta Turai ta yanke shekaru 4 da suka gabata.

Da yiwuwar dai kamfanin na Google ya sake daukaka kara kan hukuncin gaban kotun kolin Turai don kalubalantar hukuncin nay au.

Wata sanarwar kungiyar EU bayan hukuncin na kotun Lexenbourg kungiyar ta ce ya tabbata tarar da ta ci kamfanin na google na kan dai dai tana mai cewa kamata ya yi kamfanin na Amurka ya rika cikakken bayan ikan duk wani yunkuri bincike ko kuma samar da sauyi a tsare-tsarensa ga masu amfani da shi don kiyaye hakkokinsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.