Isa ga babban shafi
Sauyin yanayi

Jagororin duniya sun sha alwashin tara bilyoyin daloli don ceto dazuka

Shugabannin kasashen duniya sun sha alwashin tattara wasu biliyoyin daloli, dan yaki da sare gandun daji da kuma dakatar da shi nan da shekarar 2030.

Ana gudanar da taron sauyin yanayi na COP26 ne a birnin Glasgow na kasar Scotland
Ana gudanar da taron sauyin yanayi na COP26 ne a birnin Glasgow na kasar Scotland AP - Alastair Grant
Talla

Wannan matakin na zuwa ne bayan da kungiyoyin dake rajin kare muhalli suka sha yin kira wajen ganin an hada kai don yaki da sare gandun daji, wanda daya ne daga cikin ummul’aba’isin kwararar hamada da sauyin yanayi.

Wannan bayanin na cikin batutuwan da aka tattauna a yayin taron sauyin yanayi na COP26 dake gudana a halin yanzu, inda Birtaniya ta goyi bayan tattara biliyan 20 na dala ta hanyar gwamnatoci da bangarori masu zaman kansu.

A cewar Prime ministan Birtaniyan Boris Johnson fiye da manyan dazuka 100 na duniya ne fuskantar sara ba kakkautawa daga jama’a, wanda kuma tuni aka yiwa kaso 85 cikin dari na wadannan dazuka mummunar illa.

Cikin kasashen da suka goyi bayan wannan mataki da kuma kira da kakkarfar murya wajen tattara wadannan kudade don yaki da matsalar akwai Russia, da Brazil da Amurka da China da Australia da kuma Faransa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.