Isa ga babban shafi
COP-26

Shugabannin G20 sun jaddada matsayin yaki da sauyin yanayi

Yayin da aka bude taron sauyin yanayi na duniya da aka yiwa lakabi da COP 26 a Glasgow dake kasar Scotland, shugabannin kasashen kungiyar G20 da suka fi karfin tattalin arziki a duniya sun bayyana aniyar su ta rage dumamar yanayi da kashi guda da rabi a ma’aunin salsas.

Wakilan dake halartar taron sauyin yanayi a Glasgow
Wakilan dake halartar taron sauyin yanayi a Glasgow AFP - DANIEL LEAL-OLIVAS
Talla

Taron shugabannin kungiyar G20 na kwanaki 2 da aka gudanar a birnin Rome, ya baiwa shugabannin manyan kasashen duniyar damar jaddada alkawarin su na aiwatar da yarjejeniyar Paris ta shekarar 2015 a aikace.

Shugabannin wadanda kasashen su ke fitar da kashi 80 na sinadarin dake gurbata muhalli a duniya, sun kuma yi alkawarin takaita amfani da gawayi, ba tare sanya ranar kawar da aiki da shi gaba daya ba.

Shugabannin kungiyar G20
Shugabannin kungiyar G20 © 路透社图片

Shugaban taron kuma Firaministan Italia Mario Draghi ya bayyana matukar farin cikin su da sakamakon zaman da suka yi, wanda ya bayyana shi a matsayin matakin farko na magance matsalar da ake fuskanta.

Shugaban taron sauyin yanayin Alok Sharma ya bayyana haduwar ta Glasgow a matsayin dama ta karshe da duniya ke da ita na rage sinadaran dake haifar da matsalar sauyin yanayi.

Masu rajin kare muhalli
Masu rajin kare muhalli In Pictures via Getty Images - Mark Kerrison

Daruruwan masu rajin kare muhalli ne suka yi tattaki zuwa Glasgow domin gudanar da zanga zangar lumana da zummar kara matsin lamba ga shugabannin duniya domin ganin sun dauki mataki akai.

Ana saran shugabannin kasashen duniya su yiwa taron jawabi wajen bayyana irin matakan da kasashen su ke dauka akan matsalar sauyin yanayi, cikin su harda shugaban Amurka Joe Biden dake halartar taron a karon farko.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.