Isa ga babban shafi
EU-IRAN-NUKILIYA

Tarayyar Turai da Iran za su koma tattaunawar nukiliya a wannan mako

Wakilan Tarayyar Turai za su yi zaman tattaunawa da takwarorinsu na Tehran a cikin wannan mako a Brussels, a game da batun yarjejeniyar nukiliyar Iran, a cewar mai magana da yawun kungiyar.

Enrique Mora, mai shiga tsakani na Tarayyar Turai.
Enrique Mora, mai shiga tsakani na Tarayyar Turai. Joe Klamar AFP/Archivos
Talla

Kungiyar tarayyar Turai tare da gamayyar kasashe masu karfin arziki ne ke duba yadda za’a sake zaman tattaunawar da aka cimma a shekarar 2015 kan batun nukiliyar Tehran.

A cewar jagoran masu tattaunawar na Iran, kuma mataimakin ministan harkokin wajen kasar wato Ali Bagheri, zai kasance a Brussels ranar Larabar nan, dan ci gaba da zaman gano bakin zaren tare da sauran masu ruwa da tsaki .

Enrique Mora, wanda a cikin watan nan, ya ziyarci Tehran, yace za su yi duk mai yiwuwa, don ganin an cimma matsaya, lamarin da zai kai su ga wani zaman a vienna tare da tawagar masu ruwa da tsaki.

Yanzu dai fatan Iran da sauran kasashen ita ce na cimma matsaya kan batun nukiliyar, la’akari da yadda tsohon shugaban Amurka Donald Trump ya fice daga tattaunawar a 2018 kuma hakan ya kara jawo koma baya amma Joe Biden, ya dawo da batun tattaunawar  da darewarsa karagar mulki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.