Isa ga babban shafi
Iran-EU

EU ta musanta shirin tattaunawa kan nukiliyar Iran a Brussels

Kungiyar Tarayyar Turai ta ce ba ta da shirin gudanar da wani taro a alhamis mai zuwa don tattauna batun nukiliyar kasar Iran, sabanin yadda Tehran ta sanar.

Babban jami'in Diflomasiyyar kasashen Turai Josep Borell.
Babban jami'in Diflomasiyyar kasashen Turai Josep Borell. AP - John Thys
Talla

A wata zantawar Josep Borell da manema labarai bayan ganawarsa da ministocin wajen kasashen Turai, ya ce yana son tabbatarwa Iran cewa ba ita ke da hakkin fitar da lokacin tattaunawar ga kungiyar ba, shawara a gareta shi ne komawa mutunta yarjejeniyar maimakon ci gaba da saba mata.

Kalaman na Borell na zuwa bayan kakakin ma'aikatar cikin gida a Iran Ali Bagheri ya yi ikirarin cewa EU na shirin fara tattaunawa kan yarjejeniyar nukiliyar kasar a alhamis din makon nan a kokarin ceto yarjejeniyar wadda ke kokarin durkushewa bayan ficewar Amurka da kuma matakin Iran na fara bijirewa dokokinta.

Kungiyar kasashen Turai da ke shiga tsakani wajen farfado da tatatunawar ta ce nan bada dadewa ba take saran ganin an koma teburin tatatunawa.

An faro tattaunawar ceto yarjejeniyar ta Iran ne a birnin Vienna na Australia bayan matakin Joe Biden na amincewa da komawa cikin yarjejeniyar wadda manyan kasashen Duniya suka kulla da Iran a shekarar 2015 wadda kuma tsohon shugaba Donald Trump ya fitar da kasar a shekarar 2018.

Sai dai Amurka ta gindaya sharadin dole sai Iran ta koma ci gaba da mutunta yarjejeniyar ne tukuna za ta amince da komawa cikinta. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.