An gano ragowar gawarwakin mutanen da suka rayu shekaru 800 da suka gabata
Leburori da ke aikin shimfida bututun iskar gas a karkashin kasa sun gano wasu gawarwakin mutane 8 da masana ke kyautata zaton cewa sun haura shekaru 800 da mutuwa.
Wallafawa ranar:
Bayanai sun nuna cewa an ga gawarwakin mutanen ne manya da kanana lullube a cikin kabarin a kusa da abinci da kayan kade-kade kusa da su.
Masu binciken na kwakwaf suka ce gano irin wadannan gawarwakin bil adama da suka kwashe shekaru masu tsawo cikin kabari zai taimaka a kara gano wasu dimbin bayanai game da rayuwar mazan jiya.
Sakamakon binciken da kwararrun suka yi, ya gano cewar, mutanen 8 sun rayu ne a tsohon garin Chilca mai tazarar kilomita 60 kudu da Lima babban birnin kasar Peru.
A cikin shekarar 2019 masu binciken karkashin kasa suka gano wasu yara 227, wadanda aka yi musu gisan gilla domin tsafin gamsar da allolin da akasarin al’ummar Chimu ke bauta wa shekaru aru aru da suka gabata a Peru, a tsakanin karni na 13 zuwa 15.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu