An gano kaburbura dauke da gawarwaki da kawunan mutane a Mexico
Hukumomin kasar Mexico sun sanar da tono gawawaki 32, da kuma kawunan mutane 9, da aka binne a wasu kaburbura a Jihar Guerrero dake fama da tashin hankali.
Wallafawa ranar:
Hukumomin kasar Mexico sun sanar da tono gawawaki 32, da kuma kawunan mutane 9, da aka binne a wasu kaburbura a Jihar Guerrero dake fama da tashin hankali.
Mai Magana da yawun jami’an tsaron yankin, Roberto Alvarez, ya ce cikin gawarwakin akwai maza 31 da mace guda, kuma tuni aka kai su babban birnin Jihar Chipancingo don gudanar da bincike.
Kasar Mexico na daya daga cikin kasashen dake fama da rikicin kungiyoyi masu safarar miyagun kwayoyi, musamman a jihar Guerrero.
A watanni goma na shekarar 2016, an samu kisan kai har sau 1,832 a jihar Guerrero, inda masu bincike suka yi hasashen cewa muddin ba’a dauki mataki ba yawan samun kasha kasha zai karu da kashi 60 cikin 100.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu